ABNA24 – Ministan harkokin wajen kasar Ta Iran ya bayyana cewa; Har yanzu ana cigaba da samun kwararowar ‘ yan gudun hijira daga kasar Afghanistan zuwa cikin Iran. Har ila yau, ministan harkokin wajen na Iran ya yi isharar da yiyuwar karuwar ayyukan ta’addanci,fataucin kwayoyi da kuma tasirinsu akan wannan yankin da kuma duniya baki daya.
Bayan ga batun Afghanistan, bangarorin biyu sun kuma tattauna halin da ake ciki a kasar Yemen.
A nashi gefen, babban magatakardar MDD ya bkukaci ganin an kafa gwamnatin da za ta kunshi kowa da kowa a cikin kasar ta Afghanistan, tare da tabbatar da cewa MDD tana jaddada muhimmancin taimakawa ‘ yan gudun hijirar Afghanistan da suke cikin Iran.
Akan yakin kasar Yemen, babban magatakardar MDD ya ce; Bai kamata a ce duniya ta sa ido tana ganin yadda yaki yake cigaba a kasar Yemen din ba.
342/